Kungiyoyin Adawan Syria Sun Amince da Tsarin Shawara da Gwamnatin Assad

Hassan Abdul-Azim, shugaban 'yan adawan kasar Syria

Wakilan kungiyoyin adawa daban daban a Syria, sun amince kan tsari da za'a bi wajen gudanar da shawarwari da gwamnatin shugaba Bashar al-Assad.

Wakilan kungiyoyin adawa na siyasa da masu daukan makamai ne suka tashi daga wani taro wanda ba safai ba a ke yinshi a birnin Riyadh a jiya Alhamis, inda suka amince kan shirin ci gaba akan shawarwarin.

Duk da haka kungiyoyin basu zabi wakilansu a zaman da zasu yi da gwamnatin ba.

Shawarwarin da aka yi a kasar Saudiyya ya samo asali ne daga shirinda manyan kasashen duniya 20 suka amince akai cikin watan jiya a tattaunawar da suka yi a Vienna. Kasashen da ake kira hukumomin kasa da kasa masu goyon bayan Syria, sun ayyana watan Janairu mai zuwa a zaman wa'adin fara tattaunawa tsakanin gwamnatin Assad da kungiyoyin 'yan hamayyar kasar masu sassaucin ra'ayi.

Kamfanin dillancin labarai na kasar Saudiyya, yace kungiyoyin adawar sun "amince cewa, burin cimma yarjejeniyar ta fuskar siyasa, shine kafa kasa wacce take mutunta diyaucin 'yayanta, tsarin da anan gaba babu hanun shugaba Assad ciki."