Kwararru A Fannin Lafiya Na Gargadi Kan Cutar Coronovirus

Kwararru a fannin kiwon lafiya na ci gaba da fadakar da jama'a game da illar dake tattare da mummunar cutar nan, dake toshe hanyoyin numfashi wato Coronavirus.

Dakta Rimfa Amos, dake cibiyar binciken cututtuka da magungunan dabbobi a garin Vom dake jihar Filato, ya ce duk da a yanzu cutar bata shigo Najeriya ba, dole ne al'umma da hukumomi su dauki matakan kariya.

Kwayar cutar Coronavirus dake barazana ga rayuka, ta kuma shafi huldar kasuwanci, ilimi da sauran harkokin walwalar jama'ar kasashen da cutar ta afkawa, da masu kasuwanci da su kamar Najeriya, da 'yan kasuwarta ke zuwa kasar China sosai.

Dakta Adeyinka Adedeji, wanda likitan dabbobi ne a cibiyar binciken dabbobi a birnin Jos, ya ce alamomin cutar Coronavirus sun hada da tari, attishawa, daukewar numfashi, da sauransu, wanda sai an yi gwaji a asibiti za a iya tabbatar da cutar.

A saurari rahoto cikin sauti daga Jos a Jihar Filato.

Your browser doesn’t support HTML5

Kwararru A Fannin Lafiya Na Gargadi Kan Cutar Coronovirus