Kwayar Cutar Mura Ta "Coronavirus" Na Kara Yaduwa A Duniya

Kasar China ta ce an sami tabbacin kusan mutane 10,000 sun kamu da cutar coronavirus. Cutar ta yi sanadin mace-mace 213 a kasar in da ta fara bulla a shekarar da ta gabata.

Hukumar Lafiya ta Duniya ta WHO ta kafa dokar ta baci saboda barkewar cutar a kasashen duniya, haka zalika ta bayyana cutar a matsayin wani lamari dake bukatar maida martanin hadin gwiwa daga kasashen duniya.

Gwamnatin Shugaba Donald Trump ta gargadi Amurkawa akan kada su je China.

Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta fidda wata sanarwa akan guje wa zuwa China, bisa abin da ta kira matakin gargadi na 4. Ta kuma shawarci duk ‘yan kasar dake can su bar China.

A wani karin rahoto, yayin da ake samun labarin bullar mummunar cutar Coronavirus karon farko a yankin kasashen Larabawa, jami’an kiwon lafiya a kasashen da yawa na kokarin daukar matakan kariya daga bazuwar cutar.

Wani gidan talabijin din kasar Aljeria ya nuna yadda jami’an kiwon lafiya ke gudanar da bincike da tantance fasinjoji don duba alamun cutar ta Coronavirus a jiragen saman da su ka fito daga China ko kasashen Larabawa, inda fasinjoji da yawa daga nahiyar Asiya ke zuwa.

Dr. Hahad Amiroush, shugaban jami’an kiwon lafiya dake sa ido kan iyakoki a tashar jiragen saman Houari Boumediene dake Algiers, ya fada wa ‘yan jarida cewa fasinjojin dake tattare da hadarin cutar, wadanda ke nuna alamun masassara mai zafi, ko tari, ko kuma matsalar numfashi, za a kai su asibiti don a yi masu gwaje gwaje idan ana kyautata zaton su na dauke da cutar.

A Abu Dhabi, an sami rahoton cewa wani iyalin ‘yan kasar China ya je kasar da cutar ta Coronavirus, yayin da rahotannin kafafen yada labarai su ka ce wata jami’ar kiwon lafiya ‘yar India da ke wani asibitin kasar Saudiyya, wadda ta kamu da cutar, an maida ta kasar ta don jinya.