LAFIYA UWAR JIKI: Matakan Da Ya Kamata A Dauka Bayan Samu Juna Biyu - Kashi Na Biyu - Fabrairu 25, 2021

Hauwa Umar

A makon daya gabata shirin Lafiya Uwar Jiki ya tattauna a kan shirin da ya kamata iyaye su yi kafi mace ta samu juna biyu, kama daga lafiyar jikin ta da kuma irin sinadaren da ya kamata ace tana da su a jikin ta kafin samun ciki.

A cikin shirin na wannan makon, za a yi magana ne a kan irin matakan da ya kamata a dauka bayan samun juna biyu, domin tabbatar da lafiyar uwa da jaririn ta da kuma daukar matakan kariya ga duk wata matsala da ka iya tasowa a lokacin da mace ke dauke da ciki.

Your browser doesn’t support HTML5

LAFIYAR UWAR JIKI: Matakan Da Ya Kamata A Dauka Bayan Samu Juna Biyu - 9'56