Laifin Trump Bai Kai Girman Da Za a Tsige Shi Ba – Republicans

Sanata Lamar Alexander, R-Tenn., lokacin da yake magana da manema labarai a ranar Litinin Jan 27. Photo/Manuel…

Wasu gaggan Sanatoci ‘yan Republican sun ce, bukatar da Shugaba Trump ya mika wa Ukraine na ta binciki abokin hamayyarsa domin amfanin kansa, kuskure ne a siyasance, amma kuma ba ta kai girman da za a tsige shi ba.

Shi dai Shugaba Trump ya kwashe lokaci mai tsawo yana cewa shi bai ga abin laifi ba a wannan bukata da ya nema daga wajen shugaban Ukraine Volodymyr Zelenskiy, kan ya binciki babban abokin hamayyarsa Joe Biden a watan Yulin bara.

Trump ya kuma nemi da a yi bincike ma kan dan Biden, wato Hunter Biden wanda ya yi wa wani kamfanin gas na kasar Ukraine aiki.

Sanata Lamar Alexander na jihar Tennessee da Sanata Joni Ernst ta Iowa, sun fada a wata hira da aka yi da su cewa, lallai Shugaba Trump ya yi kuskure da ya “nemi alfarma” tare da rike kudaden tallafin soji dala miliyan 391 da aka ba Ukraine.

A karshen makon da ya gabata, aka kammala sauraren bangarorin ‘yan Republican a gaban Majalisar Dattawa da kuma na ‘yan Democrat da ke neman a tsige Trump.

Ana tuhumar shugaba Trump ne da laifin yin amfani da mukaminsa ba bisa ka'ida ba da kuma hana majalisar dokoki ta yi aikinta.

Sai dai batun a gabatar da shaidu domin su ba da bahasi a gaban Majalisar dattawa, bai kai ga gaci ba.

Hakan ya sa da dama ke ganin an kawo karshen wannan shari’a, wacce wasu ke ganin majalisar za ta wanke Trump.

Wannan ne karon farko da za a yi sharia’r tsige shugaban kasa ba tare da gabatar da shaidu a majalisar dattawa ba a tarihin Amurka.

A ranar 18 ga watan Disambar bara, Majalisar Wakilai mai rinjayen ‘yan Democrat ta tsige shugaba Trump.

Amma ga dukkan alamu, takwarar aikinta ta dattawa mai rinjayen ‘yan Republican ba za ta bi sahunta ba.