Leicester City Ta Koma Gasar Premier League

Tambarin Leicester City

Ita dai Leicester wacce ke taka leda yanzu a mataki na biyu na Premier ta kasance a gaba a teburin gasar.

Kungiyar Lecicester City ta samu dmar koma taka leda a gasar Premier League ta Ingila bayan da Leeds ta sha kaye a hannun Queens Park Rangers.

Queens Park Rangers ta lallasa Leeds ne da ci 4-0 a ranar Juma’a.

A wancan kakar wasa kungiyar ta Leicester ta fice daga matakin gasra ta Premier bayan da ta kare a uku na karshe.

Ita dai Leicester wacce ke taka leda yanzu a mataki na biyu na Premier ta kasance a teburin gaba da a gasar.