Liverpool Ta Yi Sama A Teburin Firimiya, Real Madrid Kuma Ta Yi Kasa A La Liga - 27/3/2014

Abin bai yi dadi ma Cristiano Ronaldo na Real Madrid ba, wanda yace kamar ba a son kungiyar ta lashe La Liga ne a yanzu

Kungiyar Liverpool ta koma ta biyu a teburin wasannin lig-lig na Firimiya a Ingila, bayan da ta doke Sunderland da ci 2-1. Steven Gerrard, kyaftin na Liverpool, da kuma Daniel Sturridge suka jefa kwallayen biyu. Ma’ana dai, yanzu maki daya ne tak a tsakanin Liverpool, da kungiyar Chelsea wadda take ta daya a saman teburin Firimiya.

A Spain kuma, yanzu an ture Real Madrid daga matsayi na daya a teburin La Liga, an ma ture ta daga matsayi na biyu, ta koma ta uku a bayan da ta sha kashi a hannun Sevilla da ci 2-1.

Abokiyar adawarta ta cikin birnin Madrid, Atletico Madrid, ita ce ta daya a yanzu, bayan da ta doke Granada da ci 1-0. Karin abin bakin ciki ga su ‘yan Real Madrid shi ne a yanzu babbar abokiyar tsamarsu, FC Barcelona, ita ce ta biyu a teburin na La Liga bayan da ta doke Celta Vigo da ci 3-0.

Your browser doesn’t support HTML5

Liverpool Ta Yi Sama A Ingila, Real Madrid Kuma Ta Yi Kasa A Spain - 1'00"