Lokaci Na Kurewa Na Ceto Matasa 12 Da Ke Cikin Kogo

  • Ibrahim Garba

Aikin yashe kogo don ceto yaran

Ga dukkan alamu rayuwar yaran nan da su ka makale cikin kogo mai cike da ruwa na fuskantar hadari yayin da tsarin ceto su ke dada kasancewa da sarkakkiya

Lokaci na kurewa na ceto yara 12 da kuma kocinsu na kwallon kafa, daga cikin wani kogo mai cike da ruwa da ke arewacin Thailand, a cewar hukumomin da ke sa ido kan ayyukan ceton; su na masu nuni da rashin gyawun yanayi da kuma karancin iskar shaka ta oxigen.

Yinkuri mafi girma na kai dauki da aka yi a kogon na Tham Luang Non ya kai ga rasa rai jiya Jumma'a, bayan da wani tsohon dan kundubalar ninkayar sojojin ruwan kasar ya mutu cikin ruwan. Hukumomi sun ce Mr.

Samarn Poonan na aikin girke tukwanen iskar shaka ta oxigen ga mutanen da ke cikin kogon ne, yayin da shi kuma iskar shakar tasa ta kare har ya mutu.