Mexico Ta Samu Sabon Shugaban Kasa

Andres Manuel Lopez Obrador ne sabon shugaban kasar Mexico; shi ya lashen zaben da aka yi jiya Lahadi

Andres Manuel Lopez Obrador, AMLO, dan shekara 64 da haihuwa da ya lashe zaben shugaban kasar Mexico ya yi alkawarin tunkarar gwamnatin Amurka da shugabanta Donald Trump

Andres Manuel Lopez Obrador, dan shekaru 64, mai ra’ayin sauyi, wanda kuma ya faro harkokin siyasarsa shekaru da dama da suka gabata, bayan da ya dukufa wajen kare hakkin ‘yan kasa, ya lashe zaben shugaban kasar Mexico.

A jiya Lahadi ya bayyana cewa, batun cin hanci da rashawa da kuma bin doka, na daga cikin abubuwan da gwamnatinsa za ta mayar da hankali a kai.

Wani batu kuma da gwamnatinsa za ta dukufa akai, shi ne tunkarar gwamnatin Amurka da shugabanta Donald Trump, wanda a lokacin yakin neman zabensa, ya yi ta babatun cewa zai tilastawa Mexico ta biya kudin gina katanga tsakanin kasashen biyu.

Trump har ila yau, ya kwatanta wasu ‘yan kasar Mexico a matsayin masu aikata laifuka da yin fyade idan sun tsallaka zuwa Amurka.

An dai yi ta ta-da jijiyar wuya tsakanin Mexico da Amurka, musamman dangane da yadda gwamnatin Trump ke aiwatar da tsarin “ba-sani-ba-sabo”, wanda ya kai ga raba ‘ya’ya da iyayensu, mafi aksarinsu ‘yan kasar ta Mexico akan iyakar kasar da Amurka.