Ma’abuta Kimiyya Na Rige-Rigen Neman Maganin Cutar Corona

  • Ibrahim Garba

Anan, wata ake ma allurar corona na gwaji

Yayin da rayuwar biliyoyin mutane da kuma makomar tiriliyoyin dala su ka dogara kan samun rigakafin cutar COVID-19, ma’abuta ililin kimiyya a sassan duniya na ta fadi tashin kirkiro magani mai inganci kuma mara hadari ba tare da bata lokaci ba.

Bisa kiyasi, muddun komai ya tafi daidai, duniya za ta ga maganin cikin watanni masu zuwa. Ko kuma ya zarce watanni 18. Ko kuma ma’abuta kimiyya su kasa kirkiro magani kwata kwata.

Idan ma’abuta kimiyya su ka yi nasara, zai zama wata babbar fa’ida ga duk wanda ya mallaki maganin.

“Duk kasar da ta fara kirkiro maganin ita ce za ta fara farfado da tattalin arzikinta da kuma tasirinta a duniya.” A cewar Dr. Scott Gottlieb, tsohon Kwamishinan Ma’aikatar Tantance Abinci da Magunguna ta Amurka.

A wata kasidar da ra rubuta kwanan nan a jaridar Wall Street Journal, ya ce dayake da farko dan takaitaccen adadi na magungunan ne za a samu, kasar da ta kirkiro maganin za ta fara mai da hankali ne kan bayar da maganin ga ‘yan kasa da farko.

Abin da kowace kasa ta fi bai wa muhimmanci shi ne kare ‘ya’yanta, don haka gwamnatoci za su takaita wanzar da maganin ne a cikin gida saboda amfanin yanzu da kuma tanadi saboda nan gaba. Ta yiwu ma da farko a hana fitar da maganin. Kwararru sun yi gargadin cewa ko da kuwa an kirkiro maganin, za a shafe shekaru kafin a iya samar da isasshe ta yadda sauran kasashe za su amfana.