Ma'aikatan Bankuna Sun Tsunduma Cikin Yajin Aiki A Jamhuriyar Nijar

Shugaba Mahamadou Issoufou na Jamhuriyar Nijar

Ma’aikatan bankuna na gwamnati dama na masu zaman kansu sun tsunduma cikin yajin aiki sanadiyar dimbni haraji da suke zargin an dora masu.
WASHINGTON, D.C - Ma’aikatan bankuna na gwamnati da ma na masu zaman kansu sun tsunduma cikin yajin aiki sanadiyar dumbin haraji da suke zargin an dora masu. A cewar ma’aikatan, ministoci da wasu ma’aikatan gwamnati basa biyan haraji kamar yadda aka dora masu.

Sun ce sun yi kokarin sasantawa da gwamnati amma abun ya gagara. Ta dalilin haka ne suka shiga yajin aikin kwana biyu su ga ko gwamnati zata daidaita da su.

Da alama harkokin yau da kullum sun samu tsaiko domin rashin samun kudi daga bankuna. Wakilin Muryar Amurka, Abdoulaye Mamane Amadou ya zanta da wasu da suka zo karbar kudi a bankuna domin biyan bukatunsu na yau da kullum amma dole suka hakura.

Akwai tsoron cewa kasar Nijar, wadda tana daga cikin kasashen da suka fi talauci a duniya ka iya kara shiga cikin tabarbarwar tattalin arziki. Lamarin da ka iya haddasa karuwar talauci da fatara a kasar.

Ga karin bayani daga wakilinmu Abdullahi Maman Ahmadu

Your browser doesn’t support HTML5

Ma'aikatan Bankuna sun tsunduma cikin yajin aiki