Magajin Gari Ya Ce Sakacin Na 'Yan Majalisa Ne

Magajin Garin Konni

‘Yan adawa a majalisar Birnin Konni sun nuna bakin cikinsu game da yadda lamura ke tafiya a ma’aikatar magajin garin birnin Konni, sun kuma zargi magajin garin, da yin sakaci a jagorancinsa na da’irar.

Dan majalisar da’irar birnin Konni, na bangaren jam’iyyar PNDS tarayya, Mamman Nasir Haruna, yace abin bakin cikin ne ganin yadda ake tafiyar da aiyukan birnin Konni, wanda ya hada da kasafin Kudi da kudaden shiga, kuma gashi babu wani aiki na azo a gani da aka yi.

Da yake mayarda martini Magajin garin na birnin Konni, na jami’iyyar Moden Lumana Afirka, ta Hama Amadu, yayi watsi da wannan zargi na ‘yan adawa.

Yana mai cewa “ idan sakaci ne toh na mu dukka ne” ya kara da cewa yau duk abinda yake so yayi a matsayinsa na magajin gari idan bashi da goyon bayan ‘yan majalisa aikin banza ne, idan akwai hanyoyin da suka ga cewa anyi sakaci idan suka yi Magana akai dole ne magajin gari ya amince.

Magajin gari baya aikata komai face abinda 'yan majalisar suka aminta dashi saboda haka wannan sakaci da ake batu sakacin su ne.

Your browser doesn’t support HTML5

Magajin Gari Ya Ce Sakacin Na 'Yan Majalisa Ne - 3'20"