Magajin Garin Sokoto Hassan Danbaba Ya Yi Murabus

Makadan fadar Sarkin Musulmi a Sokoto

Shi dai Magajin garin bai amince da mutuminda mai alfarma sarkin Musulmi na zaba, wai asalinsa bawa ne.

Takaddama a fadar Mai Alfarma Sarkin Musulmi Sa’ad Abubakar na uku, ya kai ga Magajin garin Sokoto, Hassan Dan-baba, yin murabus.

Rahotanni sun ce rikicin ya samo asali ne kan nadin sarautar Marafan Sokoto, da mai alfarma sarkin Musulmi Alhaji Abubakar Sa’ad na uku, ya yiwa Inuwa Abdulkadir, tsohon ministan wasannai da matasa.

Kan wannan nadin ne tsohon magajin garin na Sokoto Alhaji Hassan Danbaba, ya rubutawa Gwamnan Sokoto Aminu Waziri Tambuwal, wasika cewa Inuwa Abdulkadir, bai cancanci wannan mukami ba, domin iyayen Inuwan bayi ne.

Inuwa Abdulkadir, wanda jigo a shugabancin jam’iyya mai mulki a shiyyar arewa maso yamma, ya garzaya kotu. Amma Sarkin Musulmi ya sa baki domin a sasanta, tareda janye karar.

Rahoton yace, a zaman sulhu inda ake shirin sanya hanu kan yarjejeniyar ce, shi tsohon magajin garin Sokoton, Alhaji Hassan Danbaba, ya mike ya fice daga taron karkashin jagorancin sarkin Musulmi.

Daga bisani aka ce ya maidowa fadar sarkin musulmi, mota da al-Qur’ani, da kuma wasu kayayyaki da aka bashi a zaman Magajin garin na Sokoto.

Wakilin Sashen Hausa Murtala Farouk Sanyinna, yace duk wani yunkuriu domin jin ta bakin tsohon magajin garin, da kuma fadar mai alafarma sarkin Musulmi ya ci tura.

Your browser doesn’t support HTML5

Magajin Garin Sokoto Hassan Danbaba Ya Yi Murabus