Mahaifiyar Ado Gwanja Ta Rasu

Ado Gwanja (Hoto: Shafin Instagram na adogwanja)

Mahaifiyar Ado Gwanjo, fitaccen mawaki kuma jarumi a dandalin shirya fina-finan Hausa na Kannywood a Najeriya ta rasu.

Gwanja ya bayyana rasuwar mahaifiyar tasa ne a shafinsa na Instagram “adogwanja” a daren ranar Juma’a.

“Innalillahi wa’inna Ilaihiraju’u, Allah ya yi wa mahaifiyata rasuwa a daren Juma’a wayewar garin Asabar biyu ga watan Ramadan. Allah ya sa ta huta, Allah ya sa Aljanna ce makoma.” Gwanja ya wallafa tare da sa alamomin kuka a karshen rubutun.

Tuni dai abokanan sana’arsa da suka hada da mawaka, masu shirya fina-finai, jarumai da dumbin masoyansa suka shiga shafin nasa na Instagram suna mika ta’aziyyarsu.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto kuma sa’a biyu bayan sanar da rasuwar, mutum 1,439 sun yi tsokaci kana 3,862 sun nuna kauna ga sanarwar.