Mai Yiwuwa Daya Daga Cikin Maharan London Dan Nijeriya Ne

  • Ibrahim Garba

Wasu 'yan sanda kenan ke binciken kashe sojan na Burtaniya a titin Woolwich na birnin London.

Ana kyautata zaton a kalla daya daga cikin mutane biyun nan da su ka kashe wani sojan Burtaniya a bisa titin London dan Nijeriya ne.
Ana kyautata zaton akalla daya daga cikin mutane biyun nan da su ka hallaka wani sojan Burtaniya a kan wani titin da ke kusa da barikin soja a birnin London, dan Nijeriya ne. Ana tsammanin au Michael Adebolajo, wanda ya kammala jami'a a 2001, wanda kuma ya shiga addinin Musulunci, au dan Nijeriya ne au ya na da wata alaka da Nijeriya.

Wakilin Sashin Hausa na Muryar Amurka da ke London, Sani Dauda, ya gaya wa Aliyu Mustafan Sakkwato cewa ana kyautata zaton lallai Michael Adebolajo, wanda sunansa ma ya yi kama da na dan Nijeriya kamar yadda Aliyu ya lura, dan Nijeriya din ne. To amma Sani ya ce 'yan sanda ba su tabbatar cewa dan Nijeriya ba ne. Watakila saboda kar a sami tashin hankali tsakanin Turawa zalla da Bakaken fata da dai sauran yiwuwar matsalar bangaranci.

Sani ya ce tuni ma wata kungiyar kyamar baki ta Turawa zalla ta fara far ma masallatai. To amma ya zuwa lokacin da ya aiko da rahoton, da alamar an shawo kan lamarin.

Your browser doesn’t support HTML5

Daya Daga Cikin Maharan London Dan Nijeriya Ne?- 2:30