Majalisa Na Shirin Yin Tambayoyi Ga Bangaren Trump, 'Yan Democrat

Majalisar dattawan Amurka za ta kwashe yinin yau Alhamis tana yin tambayoyi ga lauyoyin shugaba Donald Trump da suke kare shi da kuma ‘yan majalisar wakilai da suke gabatar da karar tsige shi.

Zaman na yau na zuwa ne yayin da batun yanke shawara kan barin wasu shaidu su gabata a gaban majalisar ke kara kusantowa.

Jay Sekulow Lauyan Shugaba Donald Trump

Sai dai yadda za a kammala wannan zama cikin hanzari, ya dogara ne ga yadda ‘yan Republican da ke da rinjaye a majalisar za su amince da bukatar ‘yan Democrat kan a ji ta bakin wasu jami’an gwamnatin Trump ko akasin haka.

Wannan kuma shi ne batun da ya mamaye zaman da aka yi a jiya Laraba, a lokacin da sanatoci suka mika tambayoyinsu a rubuce.

John Bolton

Amma batun kuma da ya fi daukan hankali shi ne na tsohon mai bai wa shugaban kasa shawara kan harkokin tsaro, John Bolton.

Bolton ya rubuta wani littafi da ba a wallafa ba tukuna, inda ya yi ikrarin cewa, Trump ya fada masa ya rike dala miliyan $391na tallafin soji ga Ukraine.

Ya kuma duaki matakin rike kudaden da nufin har sai shugaban kasar Volodymyr Zelenskiy ya fito fili ya bayyana binciken cin hanci da rashawa kan abokin hamayyarsa wato Joe Biden a cewar Bolton.