Ana saura kwanaki biyu majalisar dattawa ta fara sauraron shaida don tabbatarwa da darektar hukumar leken asiri ta CIA mai riko Gina Haspel, ta shugabanci hukumar, fadar shugaban Amurka ta White House ta kare Gina cewa ita ce mace da ta cancanci wannan mukami.
Haspel dai 'yar shekaru 61 da haifuwa wacce take shugabancin hukumar a matsayin riko, tayi-tayin janye sunanta daga tantancewa saboda ta riki wannan mukami na dindindin, sakamakon damuwar da ta biyo bayan samunta da hannu a cikin wasu matakan tsananta matakan neman bayanai daga hanun fursinoni musamman wadanda ake zargi da ta'addanci, amma a cewar jami’an gwamnati, shugaba Trump na bata kwarin gwiwa cewa tayi tsayin daka.