Majalisar Dinkin Duniya na Kokarin Dakatar da Kisan Wasu Sojojin Najeriya

An Yanke Hukumcin Kisa Kan Sojojin Najeriya Saboda Bore, 17 ga Satumba, 2014 (File Photo)

Majalisar Dinkin Duniya na da Ikon yin Katsalanda a Hukuncin Kashe wasu sojojin Najeriya

A shekarar da ta gabata ne aka yanke ma wasu sojojin Najeriya hukuncin kisa bisa zarginsu da aka yi da yin bore. Abinda ya janyo hankalin Kungiyoyin kare hakkokin bil’adama da dama kuma yanzu haka ma majalisar dinkin duniya na kokarin dakatar da hukuncin.

Farfesa Abdullahi Zuru, a wata hira da yayi da muryar Amurka yace, Majalisar dinkin duniya na da ikon daukar matakan da za su dakatar da hukuncin da aka yanke ma sojojin bisa ga tsarin kudurorinta. Missali kudiri na 7 ya ba majalisar damar yin katsalanda idan suka ga hukumomi masu mulki na kokarin cin zarafin bil’adama, musamman shari’ar da ta danganci rashin adalci.

Farfesa Zuru ya cigaba da cewa Najeriya na daya daga cikin kasashen da suka rattaba hannu akan kudirin majalisar dinkin duniya na kare ‘yancin bil’adama. Wanda hakan ya ba majalisar ikon umurtar Najeriya da ta jingine hukuncin da aka yanke idan har babu adalci a shari’ar.

Bijire ma bukatar majalisar dinkin duniya na iya haifar ma kasar Najeriya ci baya a majalisar, ko kuma fidda ta daga cikin kasashen da ke da alhakin kare hakkokin bil’adama.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar dinkin duniya - 3'10"