Babban Sakataren Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya nuna girmamawa tare da mika sakon jimami ga iyalan wadanda harin 11 ga watan Satumba ya rutsa da su a Amurka.
Sakon Guterres na zuwa ne yayin da harin ta’addancin na 9/11 ya cika shekara 20.
A ranar 11 ga watan Satumbar 2001 ‘yan ta’adda suka kai hari akan tagwayen benayen cibiyar kasuwancin ta duniya, da ma’aikatar tsaron Amurka ta Pentagon da kuma Pennsylavania.
Kusan mutum 3,000 ne suka mutu a ranar ciki har da ma’aiktan kashe gobara da ‘yan sanda da suka kai dauki.
“A yau muna jimamin wannan rana wacce take ci gaba da zama a zukatan miliyoyin mutane a sassan duniya.
“Wannan ranar ce da aka rasa rayukan kusan mutum 3,000 daga kasashen 90 wadanda ‘yan ta’adda suka kasha ta hanyar ragwanci a Amurka. Sannan dubban mutane sun jikkata,”
“A wannan rana, tunaninmu na tare da wadanda wannan hari ya rutsa da su da kuma iyalansu.” Wata sanarwa da Guteress ya fitar ta ce.
A gefe guda kuma, ita ma Sarauniyar Ingila Queen Elizabeth, ta aika wa da shugaba Joe Biden sakon nuna jimamin cikar wannan hari shekara 20.
“Yayin da muke tuna zagayowar wannan rana da ta cika shekara 20, wacce aka kai munanan hare-hare a ranar 11 ga watan Satumabr 200, tunanina da addu’o’inmu na tare da iyalai da daukacin kasar, da wadanda suka tsira daga harin da kuma wadanda suka kai daukin farko.” Sarauniya Elizabeth ta wallafa a shafin Instagram din iyalan masarautar.
A shekarar 2010, Sarauniya Elizabeth ta kai ziyara inda tagwayen benayen World Trade Center suke don nuna jimaminta kan lamarin.