Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Wani Dan Sandan Ginin Majalisar Dokokin Amurka


An Kashe Wani Dan Sandan Ginin Majalisar Dokokin Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:53 0:00

An Kashe Wani Dan Sandan Ginin Majalisar Dokokin Amurka

Tun bayan farmakin da aka kai a ginin majalisar dokokin Amurka ranar 6 ga watan Janairu aka tsaurara matakan tsaro a ginin majalisar da kewaye.

Wani dan sanda da ke aiki a ginin majalisar dokokin Amurka ya mutu wani kuma ya jikkata ranar Juma’a a lokacin da wani mai mota ya afka wa wani shinge a wajen ginin majalisar dokokin.

A cewar rundunar ‘yan sandan majalisar, maharin ya fita motarsa dauke da makami ya tunkari wasu ‘yan sanda. ‘Yan sandan majalisar suka bude mashi wuta.

An bayyana cewa maharin ya mutu, abinda shugaban ‘yan sandan majalisar Yogananda Pittman ya fadawa manema labarai kenan.

‘Yan sanda sun ce sunan dan sandan da ya mutu William Billy Evans. Ya na daga cikin bangaren ‘yan sandan da ke kai daukin gaggawa kuma shekararsa 18 ya na aiki a ginin majalisar.

Shugaban Amurka Joe Biden, wanda aka yi wa bayani game da harin, a Camp David zai yi hutun karshen mako a lokacin bikin Easter. Ya kuma bada umurnin a sassauto da tutocin kasar kasa a fadar White House.

Lamarin dai ya faru ne a wajen wani wurin binciken motoci a titin Constitution Avenue, ta bangaren dakin taron ‘yan majalisar dattawa a ginin majalisar.

XS
SM
MD
LG