Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Shirya Taro Kan Tsaro

IBRAHIM K. IDRIS babban sifeton 'yansandan Najeriya

Majalisar dokokin jihar Ondo ta shirya taron karawa juna ilimi akan harkokin tsaro da suka hada da sarakunan gargajiya da 'yansanda da sojoji da shugabannin kananan hukumomi

Shugaban majalisar Dokokin jihar Onarebul Bamidele Olowoogun shi ya jagoranci taron.

Yana mai cewa duk mai wasa da harkokin tsaro yana wasa da rayuwarsa ne. Yace majalisarsa ta baiwa harkokin tsaro mahimmanci sosai.

Shi ma wakilin sojojin Najeriya dake Akure Kanar Okechukwu Samuel ya bukaci jama'a da su taimakawa jami'an tsaro. Inji shi kamata yayi jama'ar kasar kama daga kananan hkumomi zuwa kasa gaba daya su baiwa jami'an tsaro goyon bayansu.

A jawabinta kwamishaniyar 'yansandan jihar ta kira jama'a da su san yadda za'a tsara dabarun samar da zaman lafiya a jihar.

Shi ma sarkin kasar Ikaye yace sarakunan gargajiya nada rawar da zasu taka wajen tabbatar da tsaro.

A saurari rahoton Hassan Umaru Tambuwal da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Dokokin Jihar Ondo Ta Shirya Taron Tsaro - 2' 18"