Majalisar Matasan Arewa Ta Yi Zanga Zanga A Gusau

Matasa masu zanga zanga

Matasa a jihar Zamfara sun gudanar da zanga zanga a Gusau babban birnin jihar . A lokacin gudanar da zanga zangar matasan sun yi jerin gwano ne suka  nufi zauren majalisar dokokin jihar, inda suka gabatar wa majalisar korafe-korafensu a rubuce kuma a hukumance.

Munir Kaura shugaban reshen jihar Zamfara na Majalisar Matasan Arewa ya bayyana dalilansu na yin zanga zangar.

Yana mai cewa su matasa an barsu kara zube babu aikin yi basu kuma da abun yi. Bangaren ilimi inda matasan suka fi yawa ya tabarbare. Yace yau shekara uku ke nan matasan jihar ne ke zama na baya a sakamakon jarabawar kasa a duk fadin Najeriya.

Ya cigaba da cewa asibitocin jihar sun zama abun tausayi. Yace suna ji suna gani gwamnati ta dauki Naira biliyan goma da miliyan dari biyu domin gina hanya a karamar hukuma guda daya. A jihar abubuwa sun tabarbare sun kuma lalace. Yace gwamnatin da aka zaba ta siyasa kamata yayi ta kare muradun jama'a.

Akan zargin ko wasu 'yan siyasa ne suka zugasu suyi macin, Malam Munir yace suna da tasu fahimtar da ilimi da tunane da nasu muradun da kishin jiharsu saboda haka babu wanda ya turasu yin zanga zanga. Akwai alhakin mutane a kansu saboda haka dole ne suyi gwagwarmayar kwatowa jama'arsu hakkinsu.

Onarebul Dayyabu Rijiya shugaban majalisar dokokin jihar mai kula da koke-koken jama'a yana ganin zanga zangar matasan alamar cigaban jama'a ce. Yace kungiyar ita ce ta farko da ta ziyarcesu da kokensu.

Majalisar tayi alkawarin gabatar da kokensu gabanta domin yin muhawara a kai.

Ga rahoton Murtala Faruk Sayinna da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Matasan Arewa Reshen Zamfara Ta Yi Gangami a Gusau - 2' 58"