Majalisar Wakilai Zata Fara Bincike Akan Shirin Tallafawa Marasa Aiki

Shugaban Najeriya

Majalisar Wakilan Najeriya ta ce za ta fara bincike akan shirin gwamnatin Tarrayyar Najeriya na niyar tallafawa marasa ayyukan yi.

Karkashin shirin tallafin ne gwamnati ta ce zata ‘dauki malamai Dubu Dari Biyar, sannan ta baiwa matasa Mata da Maza ayyukan yi sama da Miliyan Goma a cikin ‘dan karamin lokaci. Daga dukkan alamu an kusa kaiwa shekara ‘daya da rabi tun lokacin da shugaban kasa Mohammadu Buhari ya dauki alkawarin.

Wani abu da ya dauki hankalin kwamitin tsare tsaren kasafin kudi na Majalisar Wakilai karkashin jagorancin Timothy Ngulu, yace dole ne a duba wannan tsarin sosai domin a tabbatar da cewa ba a maimaita kuskuren da aka taba yi a baya ba, da kuma tabbatar da cewa anyi aikin da ya kamata da kudin da aka fitar.

‘Yan Majalisa dai na shawartar gwamnatin Najeriya da cewa wannan shiri na da kyau, amma idan har ba tabbatar da an tsara shi yadda yakamata ba to tabbas za a tafka asara.

Mai baiwa shugaban ‘kasa shawara a fannin ayyuka na musamman Hajiya Maryam Uwais, tace ‘yan Majalisa sun amince Naira Biliyan Biyar domin wannan aiki, amma kasancewar aikin fashe fashen neman Mai da ake yi yasa an rage kudin sosai don haka zai yiwu gwamnati ta aikatar da abin da tayi niya a farko.

Your browser doesn’t support HTML5

Majalisar Wakilan Zata Fara Bincike Akan Shirin Tallafawa Marasa Aiki - 3'03"