Makarantun Tsangaya da Barace-baracen Yara Almajirai

Yaran makarantar tsangaya

Barace baracen yaran makarantun tsangaya a arewacin Najeriya da jamhuriyar Nijar ba wani abu sabo ba ne domin an dade ana yi saboda koyawa yaran saukin kai da kuma samun abun da zasu ci, sau tari kuma su ciyar da malamansu

Kamar arewacin Najeriya a kasar Jamhuriyar Nijar akan ga yara kanana da wani zibin, matasa suna yawon bara musamman bayan karewar damuna.

Wasu yaran da aka gansu suna yawon bara an tuntubesu dalilin da ya sa suna barace-barace. Wani yaron yace ya zo karatu ne amma ya fito yawon bara domin ya samu abinci. Bayan ya koshi sai ya kaiwa malaminsa sauran. Wani ma cewa yayi dole ne su fito bara su samu abun da Allah Ya basu.

Yaran tsangaya da barace barace

Shi ko wani matashi cewa yayi tun yana yaro yake zuwa neman ilimi amma sai yayi bara kodayaushe domin ya samu abinci tare da kaiwa malaminsa.

To saidai wasu iyayen yara sun yi furuci game da yawon bara da yaran su keyi. Wani yace malaman da suke kaiwa yara, da suna taimakawa malaman da ba zasu tashi su dinga yawo dasu ba daga wannan gari zuwa wancan domin neman abinci. A cewarsa iyaye ne ke da sakarci wajen kula da malaman yaransu domin idan da ana daukan nauyin malaman babu inda zasu da yaran. Rashin ba malamai tallafi ya sa suna fita da yaran. Malaman basu da abin da zasu ci balantana almajiransu idan basu yi bara ba.

Wani yace illa na tattare da barin yara kanana da basu san ciwon kansu ba zuwa yawon barace-barace. Yace wasu yaran basu da rigunan sawa ko sabulun wanka. Daga barar suke shiga wani hali daban, su shiga ayyukan asha.

Su ma malaman addinin Islama sun ce lallai barin yara kanana su yi bara a wannan lokaci bai dace ba.

Ga rahoton Haruna Bako da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Makarantun Tsangaya da Barce-baracen Yara Almajirai - 3' 36"