Manchester United Da Bayern Munich Sun Yi Kunnen Doki A Old Trafford - 1/4/2014

Bayern Munich ta kwato kunnen doki da kyar a karawar farko da Manchester United a wasannin kwata fainal na cin kofin zakarun kulob na Turai da aka kammala 'yan mintoci da suka shige a Old Traffod.

Wayne Rooney ya bugo wata kwana da Nemanja Vidic ya jefa cikin raga da kai a minti na 58 da fara wasa.

Sai dai kuma 'yan mintoci kadan a bayan da Boateng ya gwada mai tsaron gida na Manchester United, De Gea, sai Bastian Schweinsteiger ya narka kwallo a ragar 'yan Manchester United.

Za a yi karo na biyu tsakanin kungiyoyin a ranar 9 ga wata a birnin Munich.