Manjo Hamza Al-Mustapha Yana Gaida Mutanen Dake Zumudin Ganinsa a Kano

Jama'a cike da murna suna kokawar yin kusa da shi har wani ma daga carbinsa ya yi.

Al-Mustapha da shugaban kungiyar Yarbawa Dr. Fashehun cikin farar riga wanda ya rako shi tun daga Legas.Al-Mustapha ya kira Dr. Fashehun a matsayin ubansa.

Motar da Al-Mustapha ke ciki da masu yi masa rakiya.

Al-Mustapha a kan mota cikin jerin gwanon motocida da wani a kan babur a gaba.

Al-Mustapha a tsaye cikin mota kewaye da mutane yayin da shi ma yake amsa masu.

Al-Mustapha yana tsaye a cikin mota yana amincewa da gaisuwar mutanen da suka yi cicirindon tarbarsa.

Dubun dubatan jama'a da suka yi dafifi domin su ga Al-Mustapha da idanunsu yayin da ya sauka Kano.