Accessibility links

Bayan wata daya da aka sako shi daga gidan kaso inda ya kwashe shekaru goma sha hudu yana tsare gwamnatin Legas ta daukaka kara zuwa kotun kolin Nijeriya

Bayan 'yan kwanaki da Manjo Al-Mustapha ya fito daga gidan kaso inda aka tsare shi fiye da shekaru goma sha hudu sai gashi gwamnatin jihar Legas ta daukaka kara a koktun kolin Najiriya na kin amincewa da sakarsa tare da Alhaji Shofolahan da kotun daukaka kara ya yi.

Shi Manjo Al-Mustapha ya ce shigar da kara da gwamnatin Legas ta yi bai hana su yin komi ba domin haka doka ta shimfida. Ya ce su ma suna da 'yancin su bi nasu shirin a dokance kuma akan haka suma suka tsaya. Da yake mayarda martani Majo Al-ustapha ya ce ba zasu nemi fada da kowa ba domin an bata masu lokaci a kidan kaso sai dai kan wannan daukaka karar sun riga sun tuntubi nasu lauyoyin su yi abun da ya kamata.

Manjo Hamza Al-Mustapha da Alhaji Shofolahan sun kwashe kusan shekaru goma sha biyar suna tsare a kan tsarge-tsarge guda hudu da suka hada da kashe Kudirat Abiola, matar gimshakin attajirin nan kuma wanda ake harsashen shi ne ya lashe zaben shugaban kasa na shekarar 1993 da gwamnatin sojoji ta hana, marigayi Alhaji MKO Abiola.

Yayin da aka gurfanar dasu gaban sharia wani kotun magistaret na Legas ya yanke masu hukuncin kisa ta hanyar ratayewa amma kusan kwanaki talatin da bakwai da suka wuce kokun daukaka kara ta wankesu ta kuma sakesu.Kwamishanan sharia na jihar Legas ya ce suna da hujjoji takwas kan Manjo Al-Mustapha da shida kan Alhaji Shofolahan na kaukaka kara. A kan shekarun da suka bata ma Manjo suna sharia sai kwamishanan ya ce shi Manjo ne yana jan kafa wanda kuma shi kadai ya san dalilin yin hakan.

Da yake mayarda martani Manjo Al-Mustapha ya ce duk wanda ya muzgunawa mutum bisa ga karya to idan gaskiya ta bayyana dole ne ya cigaba da kage. Tun dama can kage ne. Kuma an yi anfani da kafofin labaru domin a bata masu suna amma Allah cikin ikonsa bai yarda ba. Ya ce ai basu bane suka kawo tafiyar hawainiya a shiriar ba domin a tsare suke. Gwamnatin Legas ce har ta yi anfani da alkalai goma sha hudu da magistrori guda biyu.

Ladan Ibrahim Ayawa nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG