Manoma Sun Koka Akan Farashin Takin Zamani A Nijar

Kungiyar Plate Forme Paysanne da hadin gwiwar manoma da makiyaya a jamhuriyar Nijar sun bukaci gwamnatin kasar ta dauki matakai, bayan da aka sami hauhawar farashin takin zamani a kamfanin CAIMA a wani lokaci da mazauna karkara ke gab da soma aikin damana.

Buhun takin da ake sayarwa a can da akan jikka 13.500 na CFA ya cira zuwa 16,000 inji wata sanarwar da kamfanin CAIMA mallakar gwamnatin Nijar ta fitar a baya bayan nan, matakin da kungiyar kare hakkin manoma da makiyaya wato Plate Forme Paysanne, ta ce ba za ta lamunta da shi ba bisa la’akari da yadda yake barazana ga ci gaban ayyukan noma a wannan kasa, inji shugaban wannan kungiya Djibo Bagna.

A cewar shugaban kamfanin CAIMA Mahamadou Harouna Moudi, matakin janye kudaden tallafin gwamnati daga harkokin samarda takin zamani ne mafarin tsadar farashin da aka fuskanta.

Sanin muhimmancin takin zamani ga manoma musamman mazauna karkara ya sa shuwagabanin garzayawa zuwa fadar Firai Minister Birgi Raffini, domin gabatar da kokensu, kuma a cewar kungiyar shugaban gwamnatin ta Nijar ya basu amsa mai gamsarwa.

Noma da kiwo na matsayin ayyukan da akasarin ‘yan Nijar ke dogaro akansu domin samun guzurin cimakar shekara.

ga karin bayani cikin sauti daga Souley Mumuni Barma.

Your browser doesn’t support HTML5

Manoma Sun Koka Akan Farashen Takin Zamani A Nijer - 2'44"