Manyan kamfanonin harhada wakokin zamani suna harhada wakoki da nufin tallafawa Japan

Mutanen kasar Japan da suka rasa matsugunansu sakamakon girgizar kasa da ambaliyan ruwan tsunami

kamfanonin harhada wakokin zamani suna harhada wakoki da nufin tallafawa Japan.

Manyan kamfanonin harhada wakoki na duniya guda hudu sun hada hannu wajen fitar da wadansu wakoki da zumar kafa gidauniyar tallafawa mutanen kasar Japan sakamakon girgizar kasa da kuma kazamar ambaliyar ruwa ta tsunami da aka yi wannan watan. Jerin wakokin da aka ba take “wakokin Japan” sun kunshi wakokin mutane da dama da suka hada da wakokin marigayi John Lennon, U2, Bob Dylan, Madonna da kuma Lady Gaga. Za a iya samun wakokin a hanyar nadar wakoki ta iTune a kan dala tara da santi tara, yayinda jami’an harhada wakokin suka ce za a iya samun wakokin a CD biyu farkon watan gobe. Za a mika dukan abinda aka tara ga cibiyar agaji ta Red Cross a Japan.