Martani Kan Adadin Wadanda suka Mutu A Hare-Hare Da Kisan Gilla A Najeriya

Mutane da dama su na tofa albarkacin baki a kan yawan mutanen da aka kashe cikin makonni biyun da suka shige a Najeriya a sanadin hare-haren Boko haram da na 'yan bindiga da kuma rikice-rikice na kabilanci.

Kungiyar Amnesty International mai kare hakkin bil'adama ta ce fararen hula kimanin 357 ne kungiyar Boko Haram ta kashe a wannan shekara.

Rahoton da kungiyar Amnesty International ta fitar ya zo ne a dai-dai lokacin da Najeriya, ta yi hasarar ‘yan kasar kimanin 200, a hare-haren ‘yan bindiga a jihar Zamfara, da boko haram a Mubi da kuma ‘yan bindiga a Numan ta jihar Adamawa.

‘Yan Najeriya na cigaba da mayar da martani dangane da kisan gillar da aka yiwa jama’a da dama cikin kasa da makwanni biyu da suka gabata a kasar, inda akalla mutane dari da hamsain suka rasa rayukansu a hare-hare da suka hada da na ‘yan bindiga a jihar Zamfara da kuma na boko haram a jihar Adamawa da kuma rikicin kabilanci.

A wani taron manema labarai da daya daga cikin shugabannin kungiyar ‘yan arewacin Najeriya, mazauna Legas ya gabatar, Alhaji Ado Dansoto, ya yi kira ga gwamnatin Najeriya, da ta tashi tsaye wajen ganin an kawo karshen wadannan hare-hare da ke cigaba da yawaita.

Wasu ‘yan Najeriya sun alakanta yawan kashe-kashen da ake samu a wasu sassan kasar a kowace rana da cewa yana da nasaba da siyasa kamar yadda Malam Usman Dan Zuru, bayyana.

Kashe-kashen da ke afkuwa a Najeriya, ya zo ne a dai-dai lokacin da kungiyar Amnesty International, dake kare hakkin bil’adama na kasa da kasa ta nayyana cewa ‘yan kungiyar Boko haram sun hallaka fararen hula 357 a wannan shekarar a hare-hare 55, da suka kai musamman a jihohin arewa maso gabashin Najeriya.

wakilinmu na Legas Babangida Jibrin ya duba mana wannan lamari a wannan rahoto.

Your browser doesn’t support HTML5

Martani Kan Adadin Hare-Hare Da Kisan Gilla A Najeriya