Masakar SOTEX a Jamhuriyar Nijer Na Fuskantar Barazanar Durkushewa

Hukumomi a jamhuriyar Nijer sun maida martani bayan da ma’aikatan masakar SOTEX suka koka a game da barazanar durkushewa da masana’antar ke fuskanta, lamarin da ake alakantawa da gazawar masu hannun jarin cikin gida bayan da takwarorinsu na kasar China suka janye nasu hannun jarin.

Malam Lawali Sule, mai magana da yawun ma’aikatan masakar SOTEX a lokacin da suke wani zaman dirshan da nufin tayarda mahukunta daga barci don ganin sun hamzarta bullo da matakan warware matsalolin da suka dabaibaye wannan masana’antar, yace tsawon shekara uku kenan basu sami albashi ba.

Da yake bayani a dangane da korafe korafen ma’aikatan, daraktan ofishin ministan ci gaban masana’antu Malan Mahaman Zaki ya tabbatar da cewa ma’aikatan basu sami albashi ba kuma akwai basussukan da ake bin kamfanin.

A shekarar 2017 ne hukumomin Nijer suka mayarda harkokin masakar SOTEX a hannun wani dan kasuwar cikin gida domin maye gurbin ‘yan China da suka janye nasu hannun jarin matakin da ma’aikata ke yiwa kallon mafarin tabarbarewar harkoki, abinda ya sa ofishin ministan masana’antu yunkurin shiga tsakani.

Tuni dai ‘yan rajin kare hakkin jama’a irinsu Almansour Mohamed na kungiyar CAAPAN suka fara kiran gwamnati akan maganar ceto wannan masana’antar.

Dakatar da tsarin nan na sakin marar shigo da kayan aiki ba tare da biyan kudaden awo ba da ake kira exoneration na daga cikin abubuwan da suka tilastawa ‘yan China tsinke hulda da masakar ta SOTEX wacce ainahinta gwamnatin Nijer ta kafa a shekarar 1969 da nufin gogayyar kasuwancin atamfa da takwarorinta na waje, sai dai kawo yanzu da alama haka ta kasa cimma ruwa.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Masakar SOTEX a Jamhuriyar Nijer Na Fuskantar Barazanar Durkushewa - 2'38"