Masana sun gano sauron dake sa zazzabi

Wadansu kananan yara dake jinyar zazzabin cizon sauro a asibiti

Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, kashi saba'in cikin dari na masu fama da zazaabin cizon sauro suna nahiyar Africa.
Hukumar lafiya ta duniya ta bayyana cewa, kashi saba'in cikin dari na masu fama da zazaabin cizon sauro suna nahiyar Africa. Abinda yake kara wahalar kashe kudi ga magidanta da janyo koma baya a nahiyar.

Rahoton ya bayyana cewa, kaso tamanin cikin dari dq zazzabin cizon sauro ke kashewa kananan yara ne 'yan kasa da shekaru biyar.

Kiddidiga ta nuna cewa, kowacce dakika talatin ana samun mutuwar karamin yaro guda sakamakon zazzabin cizon sauro. Zazzabin yana haddasa matsaloli ga mata masu ciki ds jarirai da suke dauke da su. Ta dalilin haka ne aka samar da wani gidan sauro da aka jika da magani.

Kwararren likita a asibitin mallam Aminu Kano, Doctor Aliyu shehu ya bayyana abubuwan dake haddasa zazzabi da yace macen sauro take daukowa, da matakan kare kai.

Wakiliyar Sashen Hausa Baraka Bashir ta aiko da rahoton daga Kano.

Your browser doesn’t support HTML5

Masana sun gano sauro dake sa zazzabi - 2:47