Accessibility links

Bullar Polio A Somaliya Na Barazana Ga Sauran Sassan Afirka


Wata ma'aikaciyar lafiya tana diga ma wani yaro maganin rigakafin cutar Polio a Mogadishu, babban birnin Somaliya

Somaliya, wadda ta shafe shekaru 6 ba a samu rahoton kamuwa da cutar Polio ko daya ba, yanzu tana fuskantar annobar Polio fiye da Najeriya

Kusan shekaru 6 ke nan ba a samu rahoton kamuwa da cutar shan inna ta Polio ko kwaya daya a kasar Somaliya ba, amma a cikin ‘yan watannin nan, sai aka ga tana yaduwa kamar wutar daji. A yanzu, Somaliya ta sha gaban Najeriya a zaman kasar da ta fi fama da annobar Polio.

A makon da ya shige kawai, an samu sabbin rahotanni har 20 na kamuwa da cutar Polio. Shirin yaki da cutar polio a duniya, (Global Polio Eradication Initiative), yace a yanzu an samu yara 73 ke nan da suka kamu da cutar ta Polio a kasar Somaliya. Idan an hada sauran kasashen duniya baki daya, yara 59 ne kawai suka kamu da cutar a wannan shekara ya zuwa yanzu.

Ma’aikatan kiwon lafiya sun damu cewar wannan cuta ta Polio tana iya samun wurin zama diris a kasar ta Somaliya mai fama da rashin kwanciyar hankali, abinda zai yi barazana ga kokarin da aka kasha dubban miliyoyin daloli ana aiwatarwa na shafe wannan cuta daga bangon duniya.

A can baya da wannan cuta ta Polio ta bulla a kasar Somaliya, ta yadu zuwa cikin kasar Yemen, daga nan ta tsallaka zuwa kasashen dake kudu maso gabashin Asiya.

Kafin wannan annobar Polio a Somaliya, an ga alamun cewa ana samun gagarumin ci gaba a yunkurin karasa wannan cuta da raba bil adama da ita a fadin duniya. A bara, yara 223 ne kawai suka kamu da cutar, watau adadi mafi kankanta da aka taba gani a tarihin wannan cuta.

A bana ma, an ga alamun cewa watakila yawan yaran da zasu kamu da cutar zai kara raguwa. Wurare kalilan da aka san har yanzu akwai wannan cuta ta Polio, sune Najeriya, musamman arewacin kasar, da Afghanistan da kuma Pakistan.

Abinda ke damun kwararrun kiwon lafiya shine akasarin yaran kasar Somaliya ba a taba yi musu allurer rigakafin wannan cut aba a saboda halin da kasar take ciki. A bayan kasar Equatorial Guinea, Somaliya ce a can kuryar baya wajen bayar da maganin rigakafin Polio a cewart Hukumar Kiwon Lafiya ta Duniya.
XS
SM
MD
LG