Masar Ta Kashe Shugaban Ajnad Misr

Jami'an tsaro inda bom ya tashi

A wani fafatawa da suka yi a tsakiyar birnin Alkahira jami'an tsaro sun kashe Hamman Muhammad Attiya na Ajnad Misr

Jami’an tsaron kasar Masar sun kashe shugaban kungiyar Ajnad Misr a wata fafatawa da suka yi a inda yake zaune cikin Birnin Alkahira.

Hamman Mohammed Attiya shugaban kungiyar an harbeshi har lahira yayinda yayi arangama da jami’an tsaro a unuguwarsa. Kungiyar bata bayar da wani sanarwa ba akan rasuwar shugaban nasu to amma bayan ‘yan sa’o’i kadan ta dauki alhakin dana bom din da ya hallaka wani jami’in ‘yansanda.

Jami’an kasar Masar sun tabbatar cewa bom din da ya tashi a wata gada dake tsakiyar Birnin Alkahira ya kuma raunata akalla mutane biyu.

Tun shekarar 2013 da sojoji suka hambarar da shugaban kasar Mohammad Morsi mai ra’ayin addinin Islama aka cigaba da kara samun hare-hare akan jami’an tsaro. Hambarar da shugaban ya biyo bayan munanan zanga zanga da ‘yan kasar suka dinga yi na nuna kin jininsa.