Masar Ta Lashe Kofin Gasar Zakarun Kwallon Kwandon Nahiyar Afirka Na BAL

Kofin gasar BAL

Zamalek ta doke takwarorinta karawarta ta US Monastir ta kasar Tunusia da ci 76-63 a gasra wacce aka watsa ta kai tsaye a kasashe da yankuna 215 cikin harsuna 15.

‘Yan wasan kwallon kwandon kasar Masar Zamalek ta zama zakarar nahiyar Afirka bayan da ta lashe kofin gasar BAL da aka yi a karon farko.

An yi gasar ce a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, wanda aka kwashe mako biyu ana yi.

Zamalek ta doke takwarorin karawarta ta US Monastir ta kasar Tunusia da ci 76-63 a gasar wacce aka watsa ta kai-tsaye a kasashe da yankuna 215 cikin harsuna 15.

Shugaban gasar ta BAL, Amadou Gallo Fall ne ya mikawa Masar kofinta, wanda hakan ke nufin an kawo karshe gasar a wannan kakar wasa.

An kuma karrama fitaccen dan wasan hukumar kwallon kwandon gasa ta NBA Hakeem Olajuwon, Dikembe Mutombo da kuma Manute Bol.

Wannan gasa ita ce ta farko da aka fara wacce aka kaddamar a ranar Lahadi 16 ga watan Mayun.

An kirkiri wannan gasa ce da hadin gwiwar hukumar kwallon Kwandon Amurka ta NBA da kuma ta kwallon Kwando ta duniya.

Kungiyoyi 12 daga nahiyar Afirka suka kara a gasar, wadanda suka hada da, Algeria, Angola, Kamaru, Masar, Madagascar, Mali, Morocco, Mozambique, Najeriya, Rwanda, Senegal da kuma Tunisia.

Wannan shi ne karon farko da hukumar NBA ta kaddamar da wata gasa a wajen yankin arewacin Amurka.