Masu Aikin Ciyar Da Daliban Firamare A Jihar Taraba Sun Koka

Yayin da a wasu jihohin Najeriya shirin ciyar da daliban makarantun firamaren da gwamnatin tarayya ta kirkiro ke samun nasara a jihar Taraba da alama kwalliya bata biyan kudin sabulu, inda wasu da aka bawa aikin ciyar da daliban da ake kira Food Vendors suka koka bisa zargin zarmiya da kuma sauya sunayensu da su ka ce jami’an kula da shirin ke yi.

Kusan karo na uku kenan da masu ciyar da daliban ke fitowa suna nuna bacin ransu akan batun, ko a kwanan baya sai da majalisar dokokin jihar ta tsoma baki a lamarin.

Matan da aka ba aikin, da suka fito daga kananan hukumomin jihar sun bukaci gwamnatin tarayya ta binciki yadda ake gudanar da shirin a jihar Taraba domin yin gyara.

Amma jami’in da ke kula da shirin, Idris Abubakar Goje, ya musanta wadannan zarge zargen da ake yi.

Shirin, na ciyar da daliban makarantar firamare ya samar da ayyukan yi ga mata dubu tamanin da bakwai, yayin da kananan yara miliyan biyu da dubu dari biyar suka amfana da shi a kusan jihohi ashirin da hudu na kasar.

A shekarar 2016 aka fara aiwatar da shirin a wasu jihohin Najeriya a karkashin kulawar Mataimakin Shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo.

Ga karin bayani cikin sauti.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Aikin Ciyar Da Daliban Firamare A Jihar Taraba Sun Koka