Masu Sassaucin Ra'ayi Sun Sami Rinjaye A Zaben Iran

Iraniyawa masu tsats-tsauran ra’ayi sun sami koma baya, a zaben da masu sassaucin ra’yin suka sami rinjaye, a zabukan da aka gudanar da suka hada da na ‘yan majalisa.

Manyan masu ra’ayin ‘yan mazan jiya biyu, Ayatollah Mohammad Yadzi da takwaransa Mohammad Taghi Mesbah-Yadzi sun sha kaye a yunkurinsu na sake zama membobin majalisar da ta kunshi malamai 88 mai matukar muhimmanci. Majalisar ce zata zabi shugabannin addinin da zai gaji Ayatollah Ali Khanemei dan shekaru 76 mai ci yanzu, wanda yake shugabanci tun shekarar 1989.

Jiya litinin tashar talabijin ta kasar ta bada labari cewa, shugaban kasar mai sassaucin ra’ayi Hassan Touhani da abokan kawancensa, sun lashe 15 daga cikin kujerun majalisa 16 a Tehran, inda ‘yan majalisa suke rike mukamin na tsawon shekaru takwas. Ga baki daya, masu sassaucin ra’ayin suna da rinjaye da kashi hamsin da tara cikin dari.