Masu Ta'aziya Sun Kama Hanyar Gombe

Gabanin isowar gawar sarkin Gombe wanda ya rasu a Landan masu ta'aziya daga birnin Abuja sun kama hanyar Gombe.
Biyo bayan rasuwar sarkin Gombe Usman Abubakar a Landan, masu ta'aziya sun kama hanyar garin gabanin isowar gawar sarkin.

Sarkin ya hau sarauta bayan rasuwar mahaifinsa a shekarar 1984.Yayi nasarar samun kirkiro jihar Gombe a shekarar 1996 lokacin milkin Abacha.

A wata zantawa da wakilin Muryar Amurka yayi da shi yayin da ya halarci taron inganta wutar lantarki a jihohin arewa da aka yi a Abuja a shekara 2010 ya tabo wasu abubuwa.

Sarkin yace kasar ta tsaya wuri daya babu abun da yake cigaba sabili da rashin ingantaciyar wutar lantarki. Lamarin ya shafi duk kasar gaba daya. Idan an zo taro a shirya hukumar da za'a dorawa alhakin kowane aiki aka tsara ba a bar tsarin kara zube ba. Abu na biye shi ne a baiwa kowace hukuma kudin aiki domin a tabbatar an yi aikin.

Dangane da sarakuna a matsayinsu na iyayen kasa, sarkin yace nasu bada shawara ne kawai. Suna yin taimako wajen sa jama'a su hada hannu da gwamnati. Misali idan gwamnati ta fada masu abun da zata yi suna iya sa jama'a su mara masu baya domin zasu fi amincewa idan sun ga sarakuna sun shiga ciki. Misali yace shi yana noma amma ba na neman abinci ba illa domin ya zama misali ga jama'a. A Najriya dole sai shugabanni sun bada misali na kwarai kafin a samu cigaba. Shugabanni su aikata abubuwa da adalci.

Sarautar Gombe na daga cikin tutocin Shehu Dan Fodio goma sha biyu a daular Sokoto da Modibbo Buba Yero ya kafa.

Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.

Your browser doesn’t support HTML5

Masu Ta'aziya Sun Kama Hanyar Gombe - 3'06"