Masu Zanga Zanga A Iran Sun Fantsama Akan Titunan Tehran

Your browser doesn’t support HTML5

Masu zanga zanga a Iran sun fantsama akan titunan Tehran da kuma wasu sauran garuruwa a rana ta biyu a jiya Lahadi, biyo bayan amincewar da gwamnatin Iran din ta yi cewa, ita ta harbo jirgin saman fasinjan Ukraine a ranar Larabar da ta gabata, wanda ya halaka mutum 176 da ke cikin jirgin.