Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus

GWAMNAN JIHAR BAUCHI BARRISTER M.A. ABUBAKAR

A jihar Bauchi mataimakin gwamnan Injiniya Nuge Gidado ya yi murabus bisa zargin nuna masa wariya da takashi a harkokin gwamnati tare da yi masa rashin yin adalci.

Alhaji Yakubu Adamu mai taimakawa tsohon mataimakin gwamnan a fannin labarai ya bayyana dalilan da suka sa mataimakin gwamnan jihar Bauchi ya yi murabus.

A cewarsa sa mataimakin gwamnan, Injiniya Nuge Gidado, ya ce gwamnan jihar bai bashi damar yin aiki yadda ya kamata ba. Kuma bai gane yadda ake tafiyar da harkokin gwamnatin jihar ba, ana yawan takashi, kuma ana yawan nuna masa wariya.

Alhaji Adamu ya ci gaba da cewa a ganin mataimakin maimakon ya tsaya ya yiwa gwamnan rashin adalci gara ya bar masa aikinsa ya yi yadda yake so.

Shi ma mai taimakawa gwamnan jihar ta bangaren ilimi da fadakar da al'umma, Alhaji Sabo Muhammad ya fadi matsayin gwamnati akan batun. Ya ce lokacin da Allah ya diba masa ne na zama mataimakin gwamna Abdullahi Abubakar ya kare. Ya ce zasu bi tsarin mulkin kasa da tsarin mulkin jama'iyyarsu ta APC su maye gurbinsa.

Ga rahoton Abdulwahab Muhammad da karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Mataimakin Gwamnan Bauchi Ya Yi Murabus - 3' 38"