A kokarinta na samarwa matasa da aikin yi, gwamnatin tarayyar Najeriya ta fara horas da matasa aikin gona kyauta.
Matasa 350 ne da suka kammala karatun manyan makarantu daga jihohi goma zasu fara amfana da wannan sabon tsarin.
An fara wannan horaswar ce a babbar kwalejin ayyukan gona ta gwamnatin tarayya dake garin Akure a cikin jihar Ondo.
Da yake bude bikin horaswar a cikin babban kwalejin aikin gona, shugaban kwalejin Dr Samson Odedina yace ana ba da wannan Horon ne a bisa umurnin Ministan Ayyukan gona da raya karkara Chief Abdu Ogbeh.
Yace ana sa ran baiwa matasan wannan horon ne domin su zamo masu dogaro da kansu, wanda za a basu jarin da zasu fara amfani da shi a matsayin share fage.
Ga Hassan Umaru Tambuwal da bayani 2’30
Your browser doesn’t support HTML5
Matasa 350 Zasu Anfana Da Horaswan Aikin Noma Kyauta