Matasa Sun Yi Zanga-zanga a Jihar Neja

Dr. Babangida Aliyu gwamnan jihar Neja

Wasu daruruwan matasa sun gudanar da zanga-zanga domin hana cigaba da aikin madatsan ruwan Zungeru wadda gwamnatin Najeriya keyi.

Madatsar ruwa da gwamnatin tarayya ke ginawa a Zungeru cikin jihar Neja da nufin samar da wutar lantarki ta haddasa zanga-zanga da daruruwan matasan yankin suka shiga yi.

Matasan sun mamaye babbar kofar shiga wurin aikin madatsar ruwan suna dauke da kwalaye masu rubucen "ku biyamu hakkokinmu". Shugaban matasan Garmai Beri yace sun zo ne su nuna cewa abun da ake yi masu basu ji dadinsa ba game da madatsar ruwan da ake ginawa. Yace shekara biyu ke nan ba'a biyasu diya ba akan filayensu da ake yin aikin. Ban da haka idan ana fasa dutse sai a fadawa mutanen dake cikin wani kauye kusa da aikin su tashi. Bayan sun gama kana mutanen kauyen su koma.

Matasan sun dauki matakin tsayar da aikin sai an biyasu kamar yadda shugaban kasa ya fada. Sai bayan an biyasu zasu bari aikin ya cigaba.

Shugaban karamar hukumar Wushishi Alhaji Umar Abubakar yayi ta fama wajen shawo kan matasan lokacin da su ke yin zanga-zangar da suka kusan share tsawon ranar Litinin suna yinta.

Alhaji Umar Abubakar yace wajibi ne su gani cewa an samu kwanciyar hankali da zaman lafiya yayin da ake yin aikin. Korafe-korafensu za'a warware. Yace idan sun yadda da shi zai dauki biyu daga cikinsu su tafi ofishin sakataren gwamnatin jihar su gabatar da bukatunsu.

Alhaji Aliyu Koshe mai taimakawa gwamnan jihar akan sake tsugunar da mutanen kauyukan da madatsar ruwan ta shafa yace bisa gaskiya ko su ma hankalinsu bai kwanta ba sabili da ko gwamnan jihar ya kan jaddada batun biyan diyan. Yace yanzu ya yiwa matasan bayani kuma sun gamsu. Kana yayi alkawarin zuwa Abuja inda zai gabatar da kukansu a biyasu domin su samu wata rayuwa ta alhaeri kada su shiga wani hali da bai kamata ba.

Tun shekarar da ta gabata shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya kaddamar da fara aikin tare da bada tabbacin cewa za'a biya diya ga al'ummomin dake zaune yankin cikin lokaci. To amma mazauna yankin sun ce har yanzu basu gani a kasa ba duk da cewa aikin ya fara nisa.

Ga rahoton Mustapha Nasiru Batsari.

Your browser doesn’t support HTML5

Matasa Sun Yi Zanga-zanga a Jihar Neja