Aware: Matasan Najeriya Sun Goyi Bayan Hada Kan Najeriya

  • Ibrahim Garba

Shugaban Awaren IPOB, Nnamdi Kanu

A cigaba da cikas din da fafatukar ballewa daga Najeriya da kungiyar IPOB ke yi, kungiyoyin matasa daga sassan Najeriya sun nuna goyon bayansu ga hadin kan kasa.

Kungiyoyin matasan kabilar Ibo da na Yarbawa da na ‘yan arewa sun tashin haikan wajen tabbatar da zaman lafiya tsakanin mabambantan al’ummomin Najeriya.

Steve Nkem Nyaka, daya daga cikin manyan Shugabannin matasan kabilar Ibo ya yaba da matakin haramta kungiyar awaren kabilar Ibo ta IPOB da gwamnonin yankin Ibo din su ka dauka. Nyaka ya bayyana goyon bayansa ga haramta IPOB din ne a wani shiri da gidan rediyon Muryar Amurka ya shirya a babban birnin Tarayyar Najeriya, Abuja.

Shi ma shugaban hadakar kungiyoyin matasan arewa, Yarima Shatima ya ce sun dago manufar jagoran ‘yan IPOB Nnamdi Kanu ta neman jawo tashin hankali a Najeriya, shi ya sa ma lokacin da su ka ga an fara takalar ‘yan aewa a kudu maso gabashin Najeriya su ka yi maza-maza su ka ruga arewa su ka kwantar da hankalin ‘yan arewa don kar su far ma ‘yan Kabilar Ibo ko wasu mutane saboda idan hakan ya faru Nnamdi zai cimma manufarsa ta wargaza kasar.

Ga Madina Dauda da cikakken rahoton:

Your browser doesn’t support HTML5

Aware: Matasan Najeriya Sun Goyi Bayan Hada Kan Najeriya