Matsalar Garkuwa Da Mutane a Najeriya Ta Ragu - 'Yan sanda

Alhaji Ibrahim Idris, Sifeto Janar na Rundunar 'Yan sandan Najeriya

A can baya matsalar garkuwa da mutane domin neman kudin fansa ta kusa zama ruwan dare gama gari a Najeriya, amma rundunar 'yan sandan kasar ta ce yanzu an samun sauki sosai.

Sai dai rundunar 'yan sandan ta ce matsalar da aka fi fuskanta yanzu ita ce ta masu shirya garkuwa da mutane na bogi.

Kakakin rundunar Jimoh Moshood ya ce akwai lokutan da mutane sukan shirya garkuwa da kansu bisa karya.

A birnin Abuja akwai wani dan siyasa kuma shahararren lauya da ya san ba zai ci zabe ba sai ya karbi kudi daga jam'iyyarsa ya kira a waya cewa an yi garkuwa da shi.

'Yan sanda sun bincika batun sun gano ba gaskiya ba ne. Haka ma wani dalibi ya yi a Gwagwalada a cewar Mashood.

A cewar Mashood dalibin wanda mahaifinsa ke aiki a wani babban banki ya hada baki da abokansa cewa an yi garkuwa da shi. lamarin da aka gano karya ne daga baya.

Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

'Matsalar Garkuwa Da Mutane a Najeriya Ta Ragu - 'Yan sanda - 1' 43"