Me Zai Biyo Bayan Tsige Shugaba Trump?

Shugaban Kasar Amurka Donald Trump

Bayan da Majalisar Wakilan Amurka ta tsige shugaba Donald Trump, kan wasu tuhume-tuhume biyu da suka yi akansa, a halin da ake ciki, babu takamaiman lokacin da aka gindaya, dangane da mika wannan matsayar ga Majalisar Dattawa.

Mataki na gaba da kundin tsarin mulkin Amurka ya shimfida idan majalisar wakilai ta tsige shugaban kasa shi ne, ta mika batun ga zauren Majalisar Dattawa a matsayin kara.

Me Zai Faru Nan Gaba?

Kafin dai Majalisar Dattawa ta himmatu kan duba wannan batu, sai Shugabar Majalisar Wakilai Nancy Pelosi, ta mika tuhume-tuhumen biyu da aka tsige Shugaban akansu ga takwararta.

An stige Trump ne bisa zargin ya yi amfani da mukaminsa domin biyan bukatun kansa.

Tuhuma ta biyu ita ce, ya janyo tsaiko ko cikas a binciken da majalisar dokokin Amurka ta yi.

Masu sharhi da dama na ganin, 'yan Democrat, sun ki bayyana matakin mika batun ga takwarorinsu na dattawa ne, domin a cewarsu, wata dabara ce da suke ganin za ta iya janyo masu goyon bayan wasu 'yan Republican.

Kuma kamar yadda masu lura da al'amura suka nuna, bayan da aka kada kuri'ar da ta amince da tsige Trump a jiya a majalisar, Pelosi ba ta nuna wata alama kan lokacin da za su mika wa Majalisar Dattawan wannan batu ba.

Amma kamar yadda rahotanni ke nunawa, abu ne mai kamar wuya, a ce 'yan Republican su tsige Trump, domin mafi aksarinsu suna goyon bayansa.

Nancy Pelosi

“'Yan Republican ba za su taba tsige shugaba Trump ba, amma dai wannan abu da ya faru, zai zama masa gargadi cikin shekara daya ko biyar da zai yi a nan gaba.” Inji Larry Sabato da ke sharhi kan siyasar Amurka.

Mitch McConnell

Shugaban masu rinjaye a Majalisar Dattawan, Mitch McConnell, ya kyankyasa cewa, batun tsige Shugaba Trump, shi ne abin da majalisar za ta ba muhimmanci a watan Janairu mai zuwa.

Sai dai faruwar hakan, zai ta'allaka ne kan lokacin da 'yan Democrat suka shigar da batun a gaban Majalisar Dattawa.