Miyyati Allah Ta Nemi Makiyaya Da Manoma Su Zauna Lafiya

Fulani makiyaya

Kungiyar Fulani Miyyati Allah ta nemi makiyaya da manoma su zauna lafiya da junansu
Kungiyar Fulani Miyyati Allah ta Najeriya ta bukaci makiyaya da manoma da su zauna lafiya da junansu su daina yin gaban kansu idan wani abu ya faru tsakaninsu.

Yayin da yake jawabi a garrin Igboho dake cikin jihar Oyo, Mataimakin shugaban kungiyar na kasa gaba daya Alhaji Ibrahim Abubakar ya kira 'yan kungiyar da su zauna cikin lumana da al'ummar jihar. Ya yi kiran ne jim kadan bayan Fulani sun kammala bikin sallah da suka saba yi kowace shekara. Ya ce idan makiyaya ya yi barna to kada manoma su dauki doka a hannunsu. Kamata ya yi su shaidawa shugabannin Fulani su yi maganin lamarin. Haka ma idan manomi ya bata wa makiyaya shi ma kada ya dauki doka a hannunsa. Ya shaidawa shugabanni.

Shugaban ya nanatawa Fulani mahimmancin makarantu. Ya ce su sa 'ya'yansu makaranta domin lokaci ya canza. Idan basu sa 'ya'yansu makaranta ba to nan gaba fa babu abun da zasi iya yi.

Shi kuwa shugaban masu saye da sayar da shanu cewa ya yi lokaci ya canza don haka idan sunga wanda basu yarda da shi ba kada su yi shiru. Su sanarda mahukunta.

Hasan Umar Tambuwal nada karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Miyyati Allah Ta Nemi Makiyaya Da Manoma Su Zauna Lafiya - 3:35