An baiwa ma’aikatan Gwamnatin Jihar Neja hutu, a daya gefen kuma Tankar Dakon man fetur ta auka cikin taron ‘yan siyasa dake yakin neman zabe a jihar, har ta Hallaka mutane biyar da jikkata wasu ashirin.
Gwamnatin jihar Neja dai ta sanar da cewa yau Alhamis da kuma gobe Juma’a, a matsayin ranar hutu ga ma’aikatanta, wannan hutu dai bai shafi ma’aikatan gwamnatin tarayya dake aiki a jihar ba, haka suma bankuna da sauran ‘yan kasuwa zasu gudanar da harkokin kasuwancinsu.
Kwamishinan yada labarai na jihar Nejan Alhaji Dan Lahdi Indayabo, yace dalilin bayarda wannan hutu shine domin baiwa ma’aikatan damar zuwa karbar katin zabensu na din din din.
A halin da ake ciki kuma gwamnatin jihar Nejan, tace ta dauki matakin cafke duk wasu masu neman tada zaune tsaye a lokacin zaben, inji antony janal kuma kwamishinan shari’a na jihar Nejan Barista Abudullahi Bawa.
A daya gefen kuma jam’iyyar adawa ta APC a jihar NeJa, ta shiga wani yanayi na zaman makoki a sakamakon yadda wata motar tankar dakon man fetur ta auka cikin wasu magoya bayan jam’iyyar ta APC, alokacin da suke kamfen a karamar hukumar Mashego, inda anan take ta hallaka mutane biyar tare da jikatta wasu mutanen sama da ashirin. Alhaji Abubakar Sani Bello da akafi sani da Abu Lolo, shine dan takarar kujerar gwamnan jihar a karkashin tutar jam’iyyar ta APC, ya tabbatar da faruwar hakan yakuma ce saboda asarar rayuka da akayi, ‘ya ‘yan jam’iyyar bazasu fita kamfen ba zasu zauna zaman makoki.
Saurari cikakken rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Your browser doesn’t support HTML5
Hutu A Jihar Neja - 2'40"