Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ankara Jawo Hankalin Matasa a Kan Bangar Siyasa


Shuwagabanin adinai
Shuwagabanin adinai

A cigaba da tattaunawar mu da wasu matasa kuma shugabanin adinai a birnin tarayyar Abuja. Daya daga cikin shugaban wata kungiyar matasan mabiya addinin kiristanci Mr. Bijinda Adamu Malik, wanda yake shugaba a wannan kungiyar a babban birnin tarayyar Abuja, ya bude filin ne da kira ga matasa da su sani fa sune gadon bayan siyasa, don haka su san da cewar babu wani abu da za’a iya yi wanda ba tare da suba. Don haka yayi kira da cewar don Allah matasa su fita suyi zabe kuma su sanar ma ‘yan uwa cewar yakamata asan wanda yakamata a zaba don bayin zaben kawai shine hakkin matasa ba, harma da zaben wanda ya kamata shima wani abub dubawa ne.

Yayi nuni da cewar matasa su tuna fa a zaben da yagabata akwai wadanda akaza ba, amma basuyi ma al’uma komai ba to don haka yakamata ayi karatun ta natsu wajen jefa kuri’a ga wadanda suka tsaya takara. Idan ansan mutun yayi alkawalin da bai cika ba to kada a zabeshi koda ko wace jam’iya yake.

Shi ma Malam. Ibrahim Mohammad Duguri, sarkin malaman Duguri kuma shugaban majalisar malamai a birnin tarayyar Abuja, yayi tushi a maganar da Mr. Bijida, yayi nacewar matasa na da rawa da zasu taka a zabe a Najeria, don haka kada su bari ayi amfani da su wajen cinma wani buri da ba zai haifarwa kasar nan da mai idoba.

Yayi kira ga matasa da suyi kokari su karbi katin su na zabe na dindindin, da hukumar zabe mai zamankanta ke rabarwa don kuri’ar ku itace ‘yancinku. Ya kuma roki matasa da a guji tashin hankali ko kuma ayi amfani dasu wajen tada zaune tsaye, kuma kada su bari abasu ‘yan kudi da kwayoyi don hargitsa zabe da muzguna ma al’umah a loacin da bayan zabe idan Allah ya kaimu.

  • 16x9 Image

    Yusuf Harande

    Yusuf Aliyu Harande, dan jarida da ke aiki da Sashen Hausa na Muryar Amurka (VOA). Yana da kwarewa a fannoni da dama, da suka hada da shafukan yanar gizo, talabijin, bincike, rubutu da hotuna. Dan asalin kauyen Hiliya ne daga karamar Hukumar Tambuwar a jihar Sakkwato.

XS
SM
MD
LG