Mr. Mulenga Sata tsohon ministan Zambia ya canza sheka zuwa jam'iyyar adawa

Shugaban Zambia Edgar Lungu

Tsohon ministan yankin Lusaka babban birnin kasar Zambia Mulenga Sata na jam’iyyar Patriotic Front mai mulki ya canza sheka zuwa babbar jam’iyyar kasar UPND a gabanin zaben kasar mai zuwa a watan Agustan bana.

Mista Sata da ne ga tsohon shugaban kasar Micheal Sata wanda kuma shine ya kafa jam’iyyar ta PF a takaice. Ya kuma taba zama minista a karkashin ofishin shugaban kasar mai ci yanzu Edgar Lungu.

Kakakin jam’iyyar adawar Cornelius Mweetwa ya bayanna cewa, sun yi maraba da samun karuwa da Mulenga, wanda yace hakan zai dada daga likkafar jam’iyyar tasu ta UPND.

Ya kara da cewa, wannan wata alama ce ta hasashen cewa jam’iyya mai mulki na durkushewa, sannan akwai yiwuwar wasu masu zaben da wadanda ba su yanke shawarar wanda zasu zaba ba su nemi shiga jam’iyyar adawar.

Masu tsokaci sun ce wannan canza shekar ba karamar koma baya ba ce ga zaben da za a sake maimaitawa na Shugaba Lungu, to amma jam’iyyar mai mulki tace ba lallai bane fitar Mista Sata ta shafi zaben da za sake ba.