Mutane 40 Sun Mutu A Tagwayen Harin Bama-Bamai Na Damuscus

Hari A Syria

Kungiyar sa'ido a Siriya tace bama bamai biyu da suka fashe a babban birnin Siriya ya kashe akalla mutane 40 sannan ya jikkata sama da 120. Harin da ya kasance mafi muni da aka kai cikin babban birnin na Siriya tun bayan shekaru 6 da fara yakin kasar.

Kungiyar sa ido kan hakkin dan adam ta Syria tace tashin bama-baman a Damascus na yau Asabar ya afku ne a yankin Bab Al-Saghir, wanda yake da manyan kaburburan ‘yan Shi’a da ke jan hankalin mahajjata ziyarar su a fadin duniya.

Maziyartan kaburburan sun taru ne a tashar mota domin ziyarar wata makabarta. Ministan harkokin wajen Iraqi yace akasarin wadanda abin ya shafa ‘yan kasar Iraqi ne. Shima Ministan cikin gida na Syria Mohammad Shaar yace harin an kai shine kan 'Yan kasashen larabawa da yawa domin kawai a kashe su.

Ya zuwa yanzu dai babu wani da ya bayyana sa hannu akan farmakin. B adai kasafai ake samun harin Bama-bamai a Damascus ba, inda anan Shugaban kasa Bashar Al’asad ya ke da karfi sosai. Kaburburan ‘Yan Shi’a na fuskantar hare-hare daga ‘yan sunni masu tsatstsauran ra’ayi a Siriya da kuma makwabciyarta Iraqi.